Zamfara ta rufe makarantu 10 sai abinda hali yayi

0

Matsalar tsaro : Zamfara ta rufe makarantu 10 sai abinda hali yayi

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnatin jihar zamfara karkashin jagoranci Gwamna Bello Muhammad ta bada umurnin rufe wasu makarantu har guda Goma da suke kan iyaka da jihar katsina sai abinda hali yayi sakamakon matsalar tsaro.

Kwamishinan Ilimi na jihar zamfara, Hon Ibrahim Abdullahi Ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani a ofishinsa, ya kara da cewa sakamakon abinda ya faru a katsina na dauke wasu dalibai a makarantun kwana a makon da ya gabata .

Yace hakan ya sanya gwamnatin jihar katsina rufe makarantun kwana na jihar, haka ya sanya gwamnatin jihar zamfara ta rufe wasu makarantun da sukayi iyaka da jihar katsina sai abinda hali yayi.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin ta rufe makarantun kwana gudana bakwai ,ta kuma rufe makarantun jeka ka dawo guda uku, Wanda suka kama makarantu guda Goma.

Ya kara da cewa cikin makarantun da aka rufe akwai GASS Zurmi da GSS Birnin magaji da GSSS Shinkafi da GSS Tsafe da GGSS Bukuyum.

Saura sun hada da GCSS Moriki sai GSSS Dansadau da GDSS Nasarawan mailayi da GSS Gusami da GSS Gurbin Bore.

Kwamishinan ya bayyana cewa ganin cewa cikin mako mai zuwa dalibai zasu tafi hutun kirsimeti don haka sukaga ya dace su rufe wadannan makarantu har sai abinda hali yayi, don kaucewa abinda kaje ya komo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here