DUK WANDA YA YI GINI A FILIN MASALLACI SAI MUN RUSHE TUNDA BA NA UWARSA BANE

0

DUK WANDA YA YI GINI A FILIN MASALLACI SAI MUN RUSHE TUNDA BA NA UWARSA BANE – KWANKWASO.

Tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya lashi takobin rushe duk wani gini da aka yi a filayen masallatan da gwamnan Kano na yanzu Abddullahi Ganduje ya sayarwa mutane.

Yayin taron rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar PDP na Kano, Kwankwaso ya nuna damuwarsa karara, kan yadda gwamnan na Kano ke yayyanka filayen masallatai yana sayarwa masu kudi.

“In ba wanda Allah ya tsinewa ba wai zai rika sayar da filin masallaci?, a jihar nan har gwamnoni kiristoci mun yi, amma ba wanda ya taba mana addini sai wanda yake ikirarin shi musulmi ne” Inji Kwankwaso.

A don haka ne yace duk wanda ya sayi filin masalaci ya kwana da sanin cewa da zarar jam’iyyar PDP ta karbi mulkin Kano za su rushe duk ginin da wadanda suka saya suka yi, “Tunda ba na uwarsu bane” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here