HARIN KANKARA; DALIBAI UKU SUN GUDO

0

HARIN KANKARA; DALIBAI UKU SUN GUDO.
@ jaridar taskar labarai
A daren jiya wasu dalibai guda uku cikin wadanda aka sace da ga makarantar kankara ta jahar katsina sun gudo.
Daliban daya daga karamar hukumar Dutsinma, daya Dan batsari dayan kuma daga kankara duk a jahar katsina.
Daya daga cikin daliban mai suna kabiru Ibrahim Wanda yake a ss1B ya fada ma uwayenshi cewa, sun lura duk masu gadin nasu sunyi barci sai suka taba wasu akan cewa su gudu.
Yace sauran daliban sunji tsoro amma su ukun su kayi ta maza , suka bar wajen a hankali suka yanki daji.
Yace bayan yini suna tafiya suka samu kansu a garin Dutsinma daga nan kowa ya kama hanyar garimsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here