KOTU TA RUSA SHUGABANCIN JAM IYYAR PDP NA JAHAR KATSINA

0

KOTU TA RUSA SHUGABANCIN JAM IYYAR PDP NA JAHAR KATSINA AMMA….
Muhammad Ahmad
@ jaridar taskar labarai
Wata babbar kotun jahar katsina mai daraja ta uku ta rushe shugabancin jam iyyar PDP na jahar katsina. A Hukuncin da ya zartar mai shara a JB bawale ya ce a sake zabe
kuma ba Wanda ya kai kara damar ya sayi fom kuma yayi takara kamar yadda kundin dokokin jam iyyar PDP ta tanada.
Karar dai ta samo asali ne, inda wani Dan jam iyyar PDP mai suna Umar Nasir Dutsinma chakis ya shigar tun a farkon shekarar nan inda yayi koken an hana shi damar yayi takara kamar yadda dokar jam iyya ta tanada.
Chakis ya Nemi da kotu ta soke duk zaben da akayi daga na jaha zuwa na kananan hukumomi.ya kuma Nemi a sake zaben da bashi dama yayi takara.
Lauyoyin chakis sun fada ma jaridun nan cewa, kotu ta basu wata damar ta hana su wadansu. Barista Tahir sagir da o.i Christopher wadanda suke tsaya ma chakis sun shaida mana cewa
Kotun ta amshi bukatar su na rusa shugabancin jam iyyar na jaha.amma kotun tace zaben da akayi na shugabancin jam iyya na kananan hukumomi da kuma na unguwanni su sunyi kuma ba wata kaidar da aka Saba, don haka suna nan daram.
Amma a zantawar da mukayi da shugaban jam iyya na jaha Wanda kotu tace ta rusa Alhaji salisu yusufu majigiri,yace suna da ja akan hukuncin,kuma zasu daukaka kara a kotun daukaka kara dake Kaduna.
Yace Dama akwai wata karar da jam iyyar ta shigar a kotun daukaka kara akan wannan shara ar , Wanda aka Sanya ranar 18/2/2020 domin sauraren ta.
Majigiri yace ana son ganin bayan PDP ne a jahar don kawai an lura ita ce mai amsar kiran talaka da fitar da shi daga halin da ya shiga.yace zamu cigaba da bin duk matakan shara a kamar yadda doka ta tanada don ganin jam iyyar ta zama lema inuwa kowa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here