TA TSERO DAGA HANNUN KINDAFAS

0

TA TSERO DAGA HANNUN KINDAFAS
daga lawal iliya batsari
Wata mata mai suna Hajia Rahane dake kauyen kufan kanawa, a gundumar yan daka,karamar hukumar batsari ta jahar katsina, ta kabuto daga hannun barayin daji masu dauke da muggan makamai.
Matar ta samu kubuta a ranar Alhamis 17/12/2020, daga inda ake tsare da ita.bayan ta kwashe kwanaki Goma sha daya a inda suke tsare da ita.
Masu garkuwa da ita, sun tafi sun barta ne, kwana biyu basu dawo ba. Data ga za a shiga kwana na uku, ta balle sarkar da aka daure ta.a jikin wani Turke ta gudo. Har Allah ya taimaka ta iso cikin jama ar gari.
Ganin halin da take ciki ga sauran sarka a kafar ta ga wahalar yunwa da ta sha, aka dauke ta zuwa asibiti batsari inda tana can ana kula da lafiyar ta..
Kalli hotunan ta da ke tattare da labarin nan.ga sauran sarkar nan a kafar ta..
________________________________________________
Ziyararci shafin katsina city news @ www.katsinacitynews.com da kuma yake a bisa duk sauran shafukan sadarwa na zamani duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here