An kaddamar da gasar wasanni ta Gida a jihar Kano
Gwamnatin jihar kano ta kaddamar da wasannin ma’aikata na gida mai taken Fedaration of Public services games karo na 39 a jihar Kano,
Sakataren gwamnati jihar Kano Usman Alhaji ne ya kaddamar gasar, a filin wasa na Kano Pillars da ke unguwar Sabon gari,
Fiye da kungiyoyin ma’aikatan gwamnati 47 ne daga hukumomi daban-daban za su fafata a wasannin na tsawon kwanaki, wanda kuma jihar Kano ce mai masaukin baki.