Sha’aban Sharada ya Kalubalanci Gwamnatin Kano akan sayar da Filaye

0

Sha’aban Sharada ya Kalubalanci Gwamnatin Kano akan sayar da Filaye

Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano da Kewaye, Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, ya ƙalubalanci gwamnatin jihar Kano akan yadda ta ke yanka filaye tare da bayar da su ga wasu masu ido da kwalli.

Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya yi wannan ƙalubalen ne a cikin wani faifan bidiyo da ya ke yawo a shafukan sadarwa na zamani.

A cikin bidiyon an jiyo muryar Sha’aban Sharaɗa na ikirarin cewa a halin da ake yanzu a jihar Kano, an yanka ko ina tare da sayarwa ga wasu masu ido da kwalli.

“An samu Masallaci an yanka ance an baiwa wane, a asibiti a yanka a ce an baiwa wane, a samu hanya a yanka an ce an baiwa wane, a samu maƙarbata a ce an yanka an baiwa wane. Me ake so? Ina za a je? Me za a yi a Duniya?”

“Wallahi billahil lazi duk wanda ya sauraramin ba ya ƙaunar Allah” In ji Sha’aban Ibrahim Sharaɗa.

Ana ganin dai Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin Sha’aban Sharaɗa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, tun bayan da aka yi zaɓen fitar da gwani na zaɓen ƙananan hukumomi inda ɗan takarar Sha’aban ɗin ya gaza kai bantensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here