Hikumar Hisbah ta jihar Kano za ta hana yin ‘fati’ da daddare
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Hukumar Hisba ta ce tana shirin hana yin bukukuwa da daddare musamman ma ‘fati’ a fadin jihar Kano, sakamakon cin karo da lokutan Sallah da galibin bukuwan ke yi.
Babban kwamandan hisba na jihar Kano Muhammad Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan ya yin ganawarsa da manema labarai a Kano.
Ibn Sina ya ce galibin ‘yan mata da suke yin biki musamman ma masu yi fatin dare na mancewa da yin sallar Magriba da kuma ta Isha’I ciki kuwa harda Amarya.
Ya ce babban abin takaicin ma shi ne galibin wuraren da ake bukuwan wurare ne da ake shan shisha da aikata al’amura marassa dadi, da masu bikin ke fakewa da shi suna barna.
“ Wanann yana tayar min da hankali, saboda yadda yaran mu da kannemu ke rayuwar abin takaici.
“Wanna abun sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihi raji’una kurum.
“Za mu fito da tsarin da duk wani irin bukukuwa da za a yi, ayi kokari ayi shi tun daga safe har zuwa karfe 4 na yamma. “Duk inda 5 tayi an rufe duk inda za a yi irin wannan bikin, wannan shi ne tsarin da muke so muyi.
Wuraren Bukakuwan Fati dai wato (Event center) na cika a birnin Kano musamman a ranakun Juma’a da kuma Asabar da Lahadi.