ANYI GARKUWA DA MIJI DA MATA A TASHAR KADANYA, BATSARI.
Daga misbahu batsari
@ jaridar taskar labarai
A daren juma’a 18-12-2020 wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, sunyi awon gaba da mata da mijin ta a kauyen Tashar Kandanya dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Maharan sun je gidan Malam Nasiru Bala inda suka tafi dashi tare da matar shi Hassana.
Majiyar mu daga bakin ‘yan uwansa sun shaida mana cewa sai bayan an tafi dashi wajen 12:30am na dare suka lura da faruwar lamarin saboda ‘yan bindigai basu yi harbi ba.
S un lababo ne ba tare da sanin kowa ba a garin. Sun bi sawun su amma dai basu iya ceto su ba domin sun riga sunyi nisa da su.
Haka kuma an labarta mana cewa anga wasu babura kirar boksa guda hudu sun tarbe su wajen kauyen Madattai inda suka dora su kan baburan suka ida isa dasu daji.
Taskar labarai ta tabbatar da cewa har yau litinin babu labarin wadannan miji da mata da aka sace.