Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Mawaki Dauda Rarara Da Frodusa Abubakar Mai Shadda.

0

DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Bayar Da Umarnin Kama Mawaki Dauda Rarara Da Frodusa Abubakar Mai Shadda.

Gidan Radiyo Freedom Kano ya rawaito cewa Kotun shari’ar musulunci da ke Kofar Kudu daura da Masarautar Kano karkashin mai shari’a Alkali Sarki Yola ta bayar da umarnin kwamushe mawaki Rarara da Abokinsa Abubakar Maishadda muddin suka ki bayyana a gabanta.

Rarara wanda Hukumar kare hakkin Bil’adama ta shigar da shi kara bisa zargin boye matar aure tare da amfani da ita a cikin bidiyon wakarsa ta ‘Jahata Ce’ wanda mijin matar mai suna Malam Abdulkadir Inuwa Indabawa ya kai musu korafi.

Wadanda suka halacci zaman Kotun sun bayyana cewa mai shari’a Sarki Yola yayi watsi da bukatar Lauyan mawakin wanda ya nemi Kotu da ta kori karar tare da ikrarin cewa ai tuni mijin matar ya sawwake mata, wanda mijin yayi inkarin batun tare da bayyana cewa a kawo hujjar da ke nuna cewa ya sake ta ko a tambayi iyayanta da waliyyinta.

Tuni dai mai shari’a Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin binciken ikrarin Lauyan Mawaki Rarara, inda Alkalin ya jadadda cewa abin da ake zargin Rararan da shi babban laifi ne a musulunci kuma muddin aka same shi da laifi dole Doka ta yi aiki a kansa. ~ Indabawa Aliyu Imam ✍️
Mun Ciro daga shafin HK TV online dake a Facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here