‘YAN BINDIGA SUN KAI HARI YANKIN BATSARI
………. Sun tafi da mutane
…………sun kwashi dukiya
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,sun bugi mutane
@ mm misbahu
@ jaridar taskar labarai
A daren jiya talata 22-12-2020 da misalin karfe 10:00pm na dare wasu mahara suka sake Kai hari kauyen Tashar kadanya dake cikin yankin karamar hukumar Batsari jahar katsina. kwanaki hudu da suka wuce sun shiga kauyen sun dauki wani magidanci da matarsa.
A harin na daren Talata sun shiga gidan wani matashin magidanci mai suna Mansir Messi, inda suka kama kanensa Rabilu da matarsa, da kanwarsa Shamsiyya, da wasu ‘yan mata dake zuwa gidan kwana masu suna Badiyya da Basira kuma duk sun tafi dasu.
Haka kuma sun bi gida gida sun kwashe suturu da sauran abin amfani da suka samu, sunyi ta harbin kan mai uwa da wabi tamkar a fagen daga.
Bayan nan sun shiga gidan wani dattijo suka tambaye shi kudi yace ba shi da ko kobo sai shanunsa ga sunan su kama.
Sai suka fadi masa cewa su ba shanu suke so ba mutane suka zo kamawa, daga karshe dai suka fita basu dauki komai ba a gidan, kuma sun lakkada ma wata matar aure dukan tsiya.
Haka dai suka ci karen su babu babbaka har tsawon awanni biyu tun goma na dare har kusan Sha biyun dare.
A wani labarin kuma duk cikin daren na jiya ‘yan bindiga sun shiga kauyen Salihawar Dan-Alhaji duk a cikin karamar hukumar batsari.inda can ma suka yayi mutane goma sha shida (16) tare da tarin shanu da tumaki.
_____________________________________________
Jaridun taskar labarai na bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma katsina city news a www.katsinacitynews.com da The links news @ www.thelinksnews.com. da sauran shafukan sada zumunta,duk sako a aiko ga 07043777779