Budurwa ta turawa saurayinta ‘Yan fashi a Kano

0

Budurwa ta turawa saurayinta ‘Yan fashi a Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kotun majistiri mai lamba 18 da ke gyadi-gyadi a jihar Kano ta ki amincewa da bada belin wata budurwa da ake zargin ta aika wa saurayinta yan fashi.

Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman a zaman kutun na yau Alhamis ya yi watsi da bukatar lauyoyinta, inda suka nemi a bada belinta da matasan da ake zargin ta aika don afkawa saurayin nata.

A kwanakin da suka gabata ne dai aka zargi budurwar mai suna Fatima Umar dake zaune a Dantsinke cikin karamar hukumar Kumbotso da aikawa saurayinta gungun matasa har su 6 dauke da makamai domin yi masa fashi saboda ya daina son ta.

Bayan duk an kammala sauraron bayanan ne Mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Disamban nan da muke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here