Mahaifin Kwankwaso ya rasu yana da shekaru 93

0

Mahaifin Kwankwaso ya rasu yana da shekaru 93

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya rasa mahaifinsa Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

Shi dai Alhaji Musa Sale Kwankwaso dake zaman Hakimin garin Kwankwaso ya rasu cikin daren wayewar garin Juma’ar nan.

Mai taimakawa tsohon Gwamna Kwankwaso a bangaren yada labarai Saifullahi Muhammad, shi ne ya wallafa rasuwar Makaman na Karaye a shafinsa na Facebook.

A cewar wani makusancin Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso Muhammad Inuwa Ali, za’a yiwa mahaifin tsohon Gwamnan Sallar jana’iza a titin Miller Road dake unguwar Bompai bayan Sallar Juma’a da misalin karfe 3 na rana.

Marigayi Alhaji Musa Sale Kwankwaso mai shekaru 93, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 19, wanda cikin su akwai mata 10 da maza 9 da kuma jikoki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here