‘YAN BINDIGA SUN SACE AMARYA DA ANGO A YANKIN BATSARI.
Misbahu batsari
@ jaridar taskar labarai
A daren ranar alhamis 24-12-2020 wasu mahara suka kai hari kauyen Bakon Zabo (Tudun modi) dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina, inda suka sace wani ango mai suna Kamala da amaryar shi Farida a gidanshi dake kauyen Tudun modi,wanda kwanaki goma sha ukku da daura masu aure.
sannan sun tsallaka gidan makwabcin angon inda can ma suka sace wata yarinyar mai suna Saadiya Haruna ‘yar aji biyu (SS II) a babbar sakandire.
kuma sun harbi mutum daya yayin da a ke dauki ba dadi dasu , domin ceto wadanda ‘yan bindiga sukayi garkuwa dasu, amma dai ba a yi nasarar amso mutanen ba.wanda aka Jima ciwo kuma yanzu haka yana asibitin batsari domin samun kulawar likita.
Duk dai a daren na alhamis yan bindiga sun shiga Saki Jiki (Bakin gulbi) inda suka bi gida gida suka sace dabbobi da suturun mutane.
sannan sun rika yin harbi kamar ana yakin kasa da kasa, amma dai basu samu wani cikas ba wajen aiwatar da ta asar ta su.
A wani labari kuma da muke samu yayin hada rohoton nan an bayyana mana harin ‘yan bindiga a kauyen Dadin Kowa duk dai cikin yankin karamar hukumar Batsari inda can ma sukayi abin da suka saba.
Duk a daren Alhamis sun kona mota kirar golf a daidai gadar Dadin Kowa.inda
Yau jumma a 25/12/2020 da rana kuma sun sace yara ‘yan mata masu tallar awara akan hanyar su ta zuwa Jibiya da suka fito daga kauyukan Batsari zasu garin Jibiya talla.
Munyi kokarin jin ta bakin yan sanda, bamuyi nasara ba