AN KAI WASU HARE-HARE A YANKIN BATSARI

0

AN KAI WASU HARE-HARE A YANKIN BATSARI.
….Wata Mata ta haifu….
Misbahu batsari
@ jaridar taskar labarai

A daren jiya asabar 26-12-2020 da misalin karfe 8:00pm na dare masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa sunkai jerin hare-hare a kauyukan Watangadiya, Biya da Garin Dodo duk a cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
A garin Watangadiya sun kai samame dauke da bindigogi amma basu yi harbi ba, sun kama mata biyu daya daga cikinsu tana goye da jinjiri, da wani namiji daya .duk cikin su babu mai wayar hannu , shi yasan ya har ya zuwa hada rahoton nan baaji duriyar su ba.
A garin Biya (Biya ki kwana) kauyen da bai wuce nisan 3km ba daga Batsari, sunyi harbe-harbe kuma sun yi garkuwa da mutane goma, namiji daya, yam mata hudu da matan aure guda biyar, daga cikin matan auren,daya ta haihu a hannun su
Wadda tana da juna biyu suka tafi da ita.
dama akwai mai juna biyu a cikin matan auren da suka dauka wacce ake tsammani tana gab da haihuwa, ‘yan bindiga da kansu suka bugo waya cewa aje aka karbo mai jegon amma a tafi da babur kirar boksa mai kyau kuma a cika tankin shi da mai (petrol).
A Garin Dodo abin ba’a magana domin sunci karen su babu babbaka da yake kauyen yana gab da dajin da suke (dajin rugu) shi yasa ma suka kama mutane kamar sunje kamen bayi domin sun yi garkuwa da mutane talatin da hudu (34).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here