An rufe Kamfanoni 2 a Kano saboda karya dokar tsabtar muhalli

0
150

An rufe Kamfanoni 2 a Kano saboda karya dokar tsabtar muhalli

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kotun tafi-da-gidan-ka kan kare tsaftar muhalli a jihar Kano ta rufe wasu masana’antu guda biyu saboda karya dokar tsaftar muhalli da ake gudanarwa a kowacce Asabar din karshen wata,

Kotun ta rufe kanfanonin robobi na NINA da Prosper Plastic, kuma an ci tarar kowannensu N500,000.

A duk asabar din karshen wata dai a Kano akan bukaci dukkan wuraren kasuwanci, kasuwanni da masana’antu su kasance a rufe har zuwa karfe 10:00 na safe.

Mai Shari’a Auwal Yusuf Suleiman wanda shi ne alkalin kotun shi ne ya yanke hukuncin yayin duba yadda aikin ya gudana a unguwar masana’antu ta Challawa dake Kano ranar Asabar.

Alkalin ya ce masana’antun sun karya tanade-tanaden sassa na 61 da na 104 na kundin dokokin tsaftar muhalli na kasa.

“Za mu bar kamfanonin su sake budewa ne kawai idan suka gabatar da rubutacciyar shaidar daga Ma’aikatar Muhalli,” inji shi.

A nasa jawabin Kwamshinan Muhalli na jihar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce kamfanonin ba sa cikin wadanda aka tsame daga tsaftar muhallin saboda yanayin ayyukan su.

kotun tafi-da-gidanka din dai ta kuma yanke wa wasu mutum 10 masu ababen hawa hukunci saboda aikata wadannan laifukan na karya dokar tsabtar muhalli a Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here