LIKEN DALOLI A BUKIN GIDAN FARFESA SANI MASHI

0
179

LIKEN DALOLI A BUKIN GIDAN FARFESA SANI MASHI
Muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Wani hoton bidiyon da jaridar katsina city news ta samu kuma ta tabbatar da inganci da sahihanci shi.bidiyon na bukin gidan farfesa sani mashi ne shugaban Hukumar Nimet ta kasa.
Ana dauki bidiyon a ranar da kayi shagalin bukin ya yansa guda uku da ya yi ma aure.wanda aka daura auren a ranar 18/12/2020.
A bidiyon an ga wata yarinya da akace diyar shi farfesa sani mashi ce, yarniyar tan lika ma daya daga cikin amaryar da ake bukin ta dalar amurka .
A farashin saye kowace dala dari ta amurka guda daya, ana sayar da ita a naira dubu arba in da takwas.( 48,000)
Jaridar ta katsina city news ta samu wannan guntun bidiyon har kala hudu na wannan dabdalar.daya mai sakan 30.dayan sakan 56.daya kuma minti daya da sakan 12.sai daya minti biyu da sakan 3.
Jaridar ta ta tuntubi farfesa sani mashi , me zai ce akan wannna dabdalar liken daloli amma duk sakon da aka aika masa babu amsa.
Mu hada wannan labarin da bidiyon mai tsawon sakan talatin 30.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here