Yansanda sun kama wanda ake zargi da yin garkuwa da dan kasar Jamus a Kano
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Rundunar yan sanda na jihar Kano sun damke wani mutum mai Abubakar Isma’il dan shekara 30 mazaunin kauyen Wangara da ke karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano,
Shafin Hausaland ya ruwaito cewa ana tuhumar Abubakar ne da Hannu wajen sace Kreser Frank Macheal Bajamushe mai shekaru 59 da ke aiki da kamfanin Dantata & Sawoe a watan Afrilun 2018.
Hakazalika ana tuhumar Abubakar Ismail wangara da adana makaman ‘yan kungiyar masu satar mutane domin karbar fansa.