AN RANTSAR DA SABBIN SHUGABANNIN KUNGIYAR GIZAGO A KANO

0

AN RANTSAR DA SABBIN SHUGABANNIN KUNGIYAR GIZAGO A KANO

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Ranar asabar da ta gabata ne kungiyar nan ta sada zumunci da raya al’adun ta Gizago wato (Gizago Social and Cultural Association) wacce ta samo asali daga jaridar Aminiya ta rantsar da sabbin shugabannin kungiyar a kasa baki daya, da ya gudana a ofishin N.U.T da ke kan titin Court Road cikin birnin Kano,

Da fari dai shugaban kwamitin zabe na kasa Malam Auwal LK ne ya fara jawabi inda ya ce kwamitin ya yi babbar nasara inda ya gudanar da karbabben zabe ga shugabanni kasa da kuma na ciyamomi a jahohi 14 na kasar nan, wanda ya gudana a rana 1-10-2020,

Auwal Lk ya kara da cewa kwamitin su ya sayar da form ga yan yantakara na 149,000 inda suka yi anfani da wasu kaso na kudin sauran aka jefa a asusun kungiya, ya ce wannan ma nasara ce, sannan ya ja hankalin wadanda aka zaba da su ji tsoron Allah kuma su yi aiki tukuru don samun nasarar kungiya,

Da ya ke nasa jawabin babban bako a wajen kuma uban kungiya Dr. Bala Muhammad ya yi kira ga shugabannin da membobi da a hada kai, domin da hadin kai ne dukkanin cigaba ke zuwa,

Dr. Bala ya kara da cewa, kamar yadda kungiya ke tara kudin Marayu ya kamata ta tara kudin taimakon aure, ya ce “muna da yan mata sun girma suna son aure, ga yan maza ma suna son aure babu hali, yin hakan zai taimakawa zumuncin kungiya, misali ace dan Ciyaman ya auri ‘yar Maaji hakan zai sa zumuncin ya dore har abada”

A jawabin sa shugaban kungiya da aka rantsar a karo na biyu. Malam Muhammad Kabir Adam Gombe ya mika sakon godiya ga dukkan Mambobin Gizago na fadin Najeriya, bisa sake sahale masa ya dare kujerar shugabancin Gizago a Karo na biyu. Sannan ya yi alkawarin cewa a wannan zango na biyu na wannan tafiyar, zai yi tsayin daka wajen ganin ya jajirce ya aiwatar da abin da ya fi na baya, domin kungiyar Gizago ta kai ga Nasara. Sai kuma ya ja hankalin Gizagawa da su zamo masu hakuri da juriya da yi wa juna uzuri da kuma bayar da hadin kai a wannan tafiya.

Barista Aminu Ibrahim Fagge ne dai ya rantsar da dukkanin shugabanni na kasa guda 32 sai kuma Ciyamomi na jahohi 14, sannan aka mika masu takardun shaida.

Taron dai ya samu halartar tsofaffin shugabanni kungiyar da membobi daga sassa daban-daban na kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here