MATA ADON GARI NI’IMAR DUNIYA

0

MATA ADON GARI NI’IMAR DUNIYA
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI yace mata su suka fi yawa a wuta.
Me kake yi wajen tseratar da kanwarka, yayarka, mahaifiyarka ko duk wacce kake da gami da ita?
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
* ANNABI yace matan dake bayyana tsiraicinsu ba za su ji koda kamshin Aljanna ba. Wanne kokari kake wajen ganin wadanda kake zagaye da su sun sanya Hijabi?
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI yace ”idan ka karantar da mace kamar ka karantar da al’umma ne” wanne kokari kake wajen ganin matan dake zagaye da kai, ka karantar da su?
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*An ruwaito cewa ANNABI yafi mace
kunya. Wanne kokari kake wajen sanyawa matan dake zagaye da kai kunya. Tun da kunya ai bangare ce daga bangarorin imani
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI yace wanda duk ya tsare ‘ya’yansa
mata daga zina har ya aurar da su zasu zame masa katanga daga shiga wuta.
Shin kana kokarin yin hakan?
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI yace dukkan mace al’aura ce sai dai
fuskarta da tafin hannayenta. Wanne kokari kake wajen ganin ka sawa matan da kake zagaye da su sun zama masu muradin kiyaye al’aurarsu.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*Mufti Isma’il Menk yace idan mace ta yi shigar banza ta fito kan titi mazinaci ne zai kulata ba mijin aure ba. To wanne kokari kake wajen ganin kanwarka mijin aurenta ne ya zo ba mazinaci ba.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI ya gargademu da cewa mu guji flower kan JUJI. Ma’ana ga kyau amma da mummuna
tsatso. Wanne kokari kake wajen ka samarwa da wacce kake da iko a kanta kyakkyawan tsatso.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*ANNABI yace idan mutumin kirki ya zo neman auren ‘yarku to ku aura masa wannan shi zai magance fitintinu. Wanne kokari kake wajen ganin ka magance wadannan fitintinun
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*An aiko ANNABI ga dukkanin maza da
mata na aljannu da mutane. Shin wanne
kokari kake wajen ganin matan da ke zagaye da kai sun tsayar da Sallah da sauran ibadu.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
*Son hakika shine duk wacce kake so da kauna kaga ka kaita Aljanna daidai kokarinka. Shin
wanne himma kake ganin ka cimma wannan burin?
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
WANNAN NASIHA CE KUMA TUNATARWA GA IYAYE MAZA, DA DUK WANI NAMIJI MAI IYA KULA DA JINSIN YAN’UWA MATA.

See also  MATSALAR RUFE KATSINA: TAKARDUN IZNI YAWO SUN YI YAWA.

Copied ?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here