Iyaye Mata Sun yi Zanga-Zanga akan Batan ‘Ya’yansu A Kano

0
396

Iyaye Mata Sun yi Zanga-Zanga akan Batan ‘Ya’yansu A Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Wasu dandazon iyaye mata sun gudanar da zanga-zanga a jiya alhamis saboda batan ‘ya’yansu da ake zargin sace su aka yi tsawon shekaru.

Matan dake dauke da takardu da hotunan yaran da suka bata sun garzaya ofishin Hukumar Karbar Korafe-korafe da Hana Cin Hanci da Rashawa (PCACC) da ma’aikatar mata don bayyana kokensu.

Mai magana da yawun masu zanga-zangar, Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce tsawon shekaru, gwamantin jihar ta nuna halin ko in kula game da damuwarsu.

A cewarta, tun daga shekara ta 2016, yara 118 ne aka sace kuma suke zargin an sayar da su ga wasu jihohin a Kudancin kasar nan.

Ta kara da cewa yawancin yaran da aka sace sun fito ne daga unguwannin Hotoro, Gama, Kawo da ‘Yankaba.

Ta ce sama da shekara daya kenan kwamitin na gwamnatin jihar Kano bai ce da su uffan ba game da lamarin batan yaran nasu.

A na ta bangaren kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar Kano Malama Zahra’u Mohamed Umar da kuma shugaban PAACC ta Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, sun tabbatarwa da iyayen cewa za a bi musu kadinsu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a baya sai da aka cafke wasu mutane da dama sannan aka gurfanar da su gaban kotu bisa zargin satar yaran, sai dai har yanzu an gaza sada yaran da iyayen nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here