RIKICIN PDP YA DAUKO SABON SALO A JAHAR KATSINA

0

RIKICIN PDP YA DAUKO SABON SALO A JAHAR KATSINA
Rikicin jam iyyar PDP ya dauko wani sabon salo mai muni a katsina inda aka dakatar da wani jigo a jam iyyar injiniya muttaqa Rabe darma .
Shugabannin mazabar wakilin kudu 1 sune sukayi taro a yammacin jiya suka dakatar dashi.shugabanni sun dogara da wani sashe na tsarin mulkin jam iyyar suka aiwatar da abin da suka shelanta.
A takardar dakatarwar dukkanin shugabannin sun sa mata hannu.in banda mutum daya.
Jam iyyar dai tana cikin rikici kala kala Wanda yanzu haka akwai shara a har guda bakwai a gaban kotu akan zaben shugabannin jam iyyar da akayi.na jahar a shekarar 2020.
Muttaqa Rabe ya rike mukamai daban daban a jam iyyar PDp kuma yana cikin wadanda suka amso mata tuta a jahar katsina a shekarar 1999. da aka kafa ta.bai kuma taba shelanta barin jam iyyar ba.tun lokacin sai yanzu da aka dakatar dashi.
Ana zargin shi da rashin biyayya ga uwar jam iyyar ta jaha

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here