Rabu da ji-ta-ji-ta, ba mu ɗaukar aiki – INEC
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da wani labari da ake yaɗawa wai ta na ɗaukar mutane aiki.
Mista Festus Okoye, Babban Kwamishina kuma Shugaban Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe na hukumar, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a ranar Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce a yanzu dai INEC ba ta ɗaukar kowa aiki, ya ƙara da cewa tun tuni aka dakatar da ɗaukar sabbin gama jami’a da ƙwararrun ma’aikata.
Ya ce: “INEC na so ta ƙara jawo hankalin jama’a zuwa ga aikin da wasu jami’an ƙarya ‘yan damfara su ke yi na ɗaukar aiki na jabu.
“’Yan damfarar sun buɗe gidajen yana na ƙaryar ɗaukar aiki inda su ke karɓar kuɗaɗe a hannun jama’ar da ba su ankara ba har su na ba su takardun kama aiki na bogi da sunan Hukumar.
“Idan za a iya tunawa, tun a ranar 30 ga Mayu, 2020, Hukumar ta bada wata sanarwa inda ta ja hankalin jama’a kan yaɗuwar wasu takardun kama aiki na ƙarya da aka ce wai sun fito daga gare ta ne.
“Mun sanar da jama’a lokacin cewa Hukumar ta dakatar da shirin ta na ɗaukar ma’aikata.
“Mun shawarci kowa da kowa da ya yi watsi da duk wata ji-ta-ji-ta game da ɗaukar aiki da raba takardun kama aiki da aka ce wai daga Hukumar ne su ka fito, kuma mun sanar da hukumomin tsaro wannan damfarar.”
Okoye ya ce wannan Hukuma dai amanar jama’a ce wadda ke gudanar da aikin ta a bisa tsarin da aka amince da shi na aiki tsakani da Allah kuma a bayyane.
Ya ce wannan tsari na yin aiki a bayyane shi ya sanya a duk lokacin da hukumar ke ɗaukar ma’aika ake yayatawa.
Okoye ya ce, “Mu an ƙara jan hankalin jama’a da su san dabarun da ‘yan damfara ke amfani da su don kada su faɗa cikin tarkon su na masu aikata laifi.”