Wani Jami’in Tsaro Ya Sadaukarda Motarsa Da Lafiyarsa Ya Kashe Dan Ta’adda
Daga: Nasir Aliyu Babanyaya
Wani jami’in tsaro na farin kaya wato DSS yayi Sanadiyyar Hallaka daya daga cikin masu Garkuwa Dashi.
Masu Garkuwan Sun shiga motar sa ne a dutsen Alhaji dake Abuja inda suka tilasa masa sai ya bisu ko su kashe shi ta hanyar nuna masa wuka, shiko da yaga bashi da wata mafita suna tafiya sai ya jefa motar rami ta gefen mai zaman banza, dama yana sanye da Seat belt, su kuma basu sanya ba, nan take motar ta juya inda tayi sanadiyyar mutuwar wanda ya sanya masa wuka, shi kuma dayan yana nan rai a hannun Allah tare da jami’an tsaro, shi kuma jami’in tsaron na DSS ya samu raunuka kadan.
Ubangiji Allah ya bashi lafiya.
Mun Ciro daga shafin Zuma times