A JARIRI DAN SATI BIYU DA MAHAIFIYARSA DAKE HANNUN YAN BINDIGA A KATSINA.
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Wannan jariri na sama sunan shi Ahmad yana da kwanaki Goma sha biyar da haihuwa, mahara miyagun daji suka kai Hari garin su, mai suna Babban Duhu dake karamar hukumar safana jahar katsina, suka tafi dashi da mahaifiyarshi mai suna lawisa yar shekaru ashirin da biyu.ita ma ga hotonta tare da wannan labarin.
Mahaifin jariri Ahmad kuma mijin lawisa sunansa Rabiu dauda matashi ne da ya gama sakandare.rashin hali ya Sanya ya kasa wucewa sai fara sana a don ya kula da iyalanshi.Baya garin lokacin da maharan suka kai Hari.yana can wani gari wajen kwadago.
Da maharan suka je garin na babban duhu sun tafi da mata Goma sha biyu.hudu daga cikin su duk suna da goyo.kuma suka tafi dasu daji.
Rabi u Dauda ya fada ma jaridun taskar labarai cewa . Wadanda suka tafi da matarsa da jaririn shi sun masa waya sun ce ya tanadi miliyan dari
Shi kuma ya shaida masu cewa bai taba ganin ko dubu dari biyu ba a hannunsa.ko tashi ko ta wani.
Dauda yace sun kara kiranshi suna neman miliyan talatin, yace sai nace masu a in za a hada abin da kowa ya ke dashi a duk fadin babban duhu baya kaiwa miliyan talatin.
Yanzu haka wannan jaririn da mahaifiyarshi sun kwashe kwanaki Goma sha daya a daji hannun wadannan mahara.suna tare da mata Goma sha biyu.
Wadanda abin ya shafa sun bude gidauniyar neman taimako suna tarawa don samun wani abu mai kauri da su ba maharan su sako masu iyalinsu.kamar yadda aka shaida ma jaridun taskar labarai.
______________________________________________
Jaridar taskar labarai na bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta. Tana da yan uwa jaridar katsina city news dake a www.katsinacitynews.com da kuma the links news dake a www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga 07043777779