Hukumar Hisbah ta jihar Kano za ta fadada yawan ofisoshinta
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Babban Kwamandan hukumar ta jihar Kano, Harun Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara ofishin hukumar dake rukunin gidaje na Sheikh Nasiru Kabara, wanda aka fi sani da (Amana).
Babban Kwamandan ya ce, “Shirye-shirye sun yi nisa wajen fadada yawan ofisoshinmu kuma a sabuwar shekarar nan da karfinmu za mu dawo aiki.
“Abubuwa suna tafiya yadda ya kamata, kuma za mu tabbatar da an gina ofis a sabbin unguwannin Kano, don yaki da bata gari,” cewar Ibn Sina.
Ya kara da cewa, za a tabbatar da gina karin ofisoshinta a dukkan lungu da sako na jihar.
Sannanan ya ce, ta haka ne kawai hukumar za ta samu saukin yaki da bata-gari a jihar Kano.