AN KARA KUBUTAR DA MUTANE 37 DAGA WAJEN MASU GARKUWA A JAHAR KATSINA

0
145

AN KARA KUBUTAR DA MUTANE 37 DAGA WAJEN MASU GARKUWA A JAHAR KATSINA

Da yammacin yau Juma’a 08/01/2021 aka kara amsar mutane talatin da bakwai (37) da aka kubutar dasu daga hannun masu garkuwa da mutane, Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin tsaro Alh. Ibrahim Katsina shine ya amshi mutanen Amadadin Gwamnatin Jihar Katsina.

Da yake zantawa da manema labarai a wurin amsar mutanen, Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara Alh. Ibrahim Katsina ya bayyana “cewa, kubutar da mutanen yana cikin kokarin samar da zaman lafiya a Jihar Katsina. Cikin sati daya an kubutar mutane (141) daga hannun masu garkuwa da mutane, Sannu a hankali sai an kubutar da duk mutanen da suke hannun masu garkuwa da mutane, kuma daukar mutanen ma ayi garkuwa dasu saiya zama tarihi da yaddar Allah.

Alh. Ibrahim Katsina ya cigaba da “cewa kokarin amsar mutanen daga hannun masu garkuwa da mutane, hadin gwiwa ne da shugabannin Al’ummar Fulani, da Gwamnatin Jihar Katsina da Jami’an tsaro, an kubutar da mutanen ba tare da bada kudin fansa ko sisin kobo ba, Suda kansu fulanin dajin suka nemi a sasanta a samu zaman lafiya, don sun kaji da yadda sunan kabilar fulani yake baci a duniya a halin yanzu. Wannan itace hanyar da akebi wajen kubutar da mutanen.

Daga cikin mutanen da aka kubutar, kuma Mobile Media Crew ta zanta dasu, harda wani Maigari na Garin Bakon Zabo dake yankin karamar hukumar Batsari, sai wata Amarya da Angonta suma yan Garin Bakon Zabon, wanda lokacin da aka dauke su basu wuce kwana goma dayin aure ba, sauran mutanen aka kubutar sun hada da mata da kananan yara.

Da yake isar da sakon Maigirma Gwamnan Jihar Katsina ga mutanen da aka kubutar, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa ya bayyana “cewa Mai girma Gwamna yana baku hakuri da kuma jajanta maku, Allah ya kiyaye abkuwar haka a gaba, ya kuma yi kira gareku daku cigaba da addu’a Allah kawo mana karshen wannan masifa, sakataren Gwamnatin ya cigaba da cewa likitoci zasu zo su duba lafiyar ku, bayan nan akwai wani dan tallafi da za’a baku ku rike ku isa dashi gida.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
08, January 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here