YAN SANDA SUN SAKE GAYYATAR MAHADI SHEHU

0

YAN SANDA SUN SAKE GAYYATAR MAHADI SHEHU
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Rundunar yan sanda ta kasa dake Abuja ta sake gayyatar sannan mai kwarmaton nan Dan asalin katsina mazaunin Kaduna, Alhaji mahadi shehu
Jaridar taskar labarai ta samu wata takarda,daga wata majiya a hedkwatar rundunar yan sanda ta kasa dake Abuja.
Takardar an rubuta ta a ranar 4 ga watan Janairu 2021 inda yan sanda suka rubuta ma.lauyan mahadi shehu mai suna Abubakar almustafa esq.
Takardar wadda ke da taken , wasikar gayyata.a cikin wasikar an tuna ma lauyan cewa an ba mahadi shehu belin kansa da kansa bisa cancantarsa.kuma aka bukaci ya kawo kansa a ranar litinin 21ga watan disamba 2020.amma mahadi shehu bai zo ba, bisa dalilai na cutar covid 19.
A cigaban wasikar akace don haka yanzu ana bukatar mahadi shehu ya kawo kansa da kansa a ranar litinin 11/1/2021.da karfe sha biyu na Rana.
In kuma zai zo ya taho da takardun da ake binciken sa akansu.da kuma bayanan likita na cutar covid 19 da ta hana shi zuwa a ranar 21/12/2020. Don mu samu damar kammala binciken mu.inji yan sanda a takardar
Jaridar taskar labarai ta samu tabbacin an kaiwa lauyan Mahdi shehu wannan takardar gayyatar ,amma bamu samu tabbacin ko ta iske mahadi shehu ba shi da Kan kansa.
Tun a cikin shekarar 2020 malam Mahdi shehu ke fallasa da fitar da sakonnin bidiyo ta yanar gizo akan gwamnatin jahar katsina.na zarge zarge daban daban, A sakon shi ya fitar da daruruwan takardu akan gwamnatin.takardun da babu wata hukuma ko kungiya mai zaman kanta da ta bincika ta tabbatar da inganci ko rashin sahihancinsu.
Karshen shekarar data gabata gwamnatin katsina ta shigar da korafi ga hukumar yan sanda ta kasa.akan haka aka tsare ,malam mahadi shehu tsawon kwanaki daga baya aka sake shi.shine yanzu aka sake gayyatar shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here