Kannywood: Babban burina shi ne na cika da Imani–Ibrahim Mandawari

0

Kannywood: Babban burina shi ne na cika da Imani–Ibrahim Mandawari

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Daya daga cikin iyayen masana’antar Kannywood Ibrahim Mandawari ya bayyana cewa har yanzu yana fitowa a Finafinai na masanaartar Kannywood,

Mandawari ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya kara da cewa jaruman da ya fi jin dadin fitowa da su a Fim su ne Hauwa Ali Dodo da kuma Hauwa Maina wadanda dukkaninsu sun rasu,

Ya kara da cewa ya fi so ya fito a matsayin mai kwatar yanci, sannan kuma abinda ya fi ki shi ne ya fito a matsayin mai zalumtar mata ko kuma kananan yara,

Ibrahim Mandawari wanda shi ne mai unguwar Mandawari ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne, ya ga ya cika da Imani, a yanzu haka dai shi ke shugabantar kungiyar raya Al’adu Hausa mai suna Waiwaye a don tafiya da ke bikin shekara shida da kafuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here