RIKICIN DAYA DABAIBAYE SARAUTAN  MADAKIN ZAZZAU TUN DAGA 1804-2020

0

RIKICIN DAYA DABAIBAYE SARAUTAN  MADAKIN ZAZZAU TUN DAGA 1804-2020

*(1)* Sarautan Madakin Zazzau ta samo asali ne tun daga Mulkin Habe.Kuma duk wanda akaba ana sa ran zai zama Sarki.

*(2)* Sarautace wacce take matsayin kwamandan rundunan sojojin masarauta a wancan lokacin.Duk mayaka suna karkashin Madaki ne; shiyasa Mafi akasari Yayan Sarki me ci ake ba.Kuma takan zama kaman kowane hakimi yana karkashin Madaki.

*(3* ) Da mulkin fulani yazo sai suma suka cigaba da anfani da ita kaman yadda Habe sukeyi duk da cewa an sami yan banbanci.

( *4* )Wuni abun mamaki ga sarautan Madaki shine tun daga 1804 har zuwa 2021 a zazzau itace Sarauta mafi daraja bayan Sarki.

(5)* Sarkin Zazzau Mallam Musa shine ya fara nada Sarkin Zazzau Yamusa Madakin Zazzau.

*(6)* Sarkin Zazzau yamusa ya nada ” *Jaye* ” Madakin Zazzau badan shi yamusan yanaso ba sai dan yaji tsoron kar Jaye ya yakeshi.

*(7)* Rasuwan Jaye keda wuya Sarkin Zazzau yamusa ya nada dansa *Hammada* Madakin Zazzau.

*(8)* Da sarkin Zazzau Abdulkarimu ya zama Sarki yayi maza-maza ya tube Hammada daga Sarautan Madaki ya kuma maye gurbinsa da *Abubakar* dan Sarkin zazzau Mal.Musa.Wanna n wuni yunkuri ne na raba kan gidan sarautan mallawa.

*(9)* Sarkin zazzau Muhammadu sani na Zama sarki ya wankacalar da Madaki Abubakar daga Sarautan Madaki ya kuma maye gurbinsa da dansa.

*(10)* Da Sarkin Zazzau Sidi Abdulkadir ya zama Sarki ya nada *Abdullahi* dan Sarkin Zazzau Hammada Sarautan Madakin Zazzau.Abinda ya zamo wuni cika alkawari dashi Sarkin zazzau sidi Abdulkadir yayi da Sarki Hammada.

*(11)* Sarkin Zazzau Abdulsalami yabar Madakin zazzau Abdullahi a sarautansa.Bai cire shiba har ya gama Mulki.

*(12* ) Zamowan Madakin Zazzau Abdullah Sarkin Zazzau keda wuya yayi wuf ya nada dansa *usman* *yero* Madakin zazzau.Hakan da yayi ya nuna ya gaji Kakansa Yamusa wajan dasa yayansa akan sarauta.Domin hakan yanuna cewa Sarki Abdullahi yanason dansa Usman yero ya gajeshi.

*(13)* Hawan Sarkin zazzau Abubakar keda wiya karagan Mulki ya tunbuke Usman yero a matsayin Madakin zazzau ya kuma maye gurbinsa da *Ali* dan Sarkin zazzau Mal.Musa.

*(14* ) Wuni abin mamaki anan shine yadda sarakunan mallawa uku kenan da sukayi sarki amma babu wanda ya nada dansa Madakin Zazzau

*(15)* Dawowan Sarki Abdullahi karagan Mulki ya sake Maido da dansa Usman yero a matsayin Madakin Zazzau.

*(16)* Sarkin Zazzau Sambo na hawa kan Sarautan Zazzau ya tube Usman yero a Madaki ya nada *Anu* dan Sarkin Zazzau Yamusa a matsayin Madakin Zazzau.

See also  Kwalastirol | Nawa ne adadin ƙwan da zan ci ba matsala?

*(17)* Bayan wuni lokaci Sarki Sambo ya tube Madaki Anu ya kuma maye gurbinsa da dansa *Lawal* a matsayin Madaki.

( *18)* Duk wannan kai- kawo da akeyi akan Sarautan Madaki anayi ne don Wanda aka ba ya zama Sarki.

( *19)* Zamowan Usman yero keda wuya sarautan Zazzau yayi maza-maza ya nada dansa.lawal *kwasau* Madakin zazzau.

( *20)* Abin dai cigaba yayi domin Lawal kwasau ma yana zama Sarki shima ya nada dansa *Ibrahim* Madakin Zazzau.

( *21* )Sarki Alu dan Sidi shima ba’a barsa a baya ba domin yana Zama Sarki shima kawai yayi- wuta-wuta ya fancakalar da Madakin Zazzau Ibrahim dan Kwasau baiyi sanya ba ya maye gurbinsa da dansa Madaki *Sa’idu* .

(22) Sarki Alu ya cire Madaki Sa’idu ya kuma Maye gurbinsa da wuni dansa Madaki *yero* wanda shima dai daga baya an cireshi.Ance Alu ya sake dawo da Madaki Sa’idu

*(23)* Tarihi ya nuna cewa Sarkin Dalhatu yana kulle da Sarki Alu dan Sidi; don haka Dalhatu na zama Sarki yayi waje da Madaki Sa’idu ya kuma maye gurbinsa da dansa *Abdu* (Madaki Abdu) bai jimaba ya rasu.Sai Sarki Dalhatu ya sake nada dansa *Shehu* a matsayin Madakin Zazzau

*(24)* Koda Sarkin Zazzau Ibrahim dankwasau ya zama Sarki Madaki shehu yaci gaba da zama a Madakin Zazzau domin kani yake a wajan sa.Domin da Sarki Dalhatu uban Madaki shehu da Sarki Lawal kawasau duk yayan Sarkin Zazzau Abdullahi ne.Bahaushe yace tuwona maina.

*(25)* Madaki shehu ya cigaba da Zama Madakin Zazzau har a lokacin Sarkin zazzau Jafaru dan Isiyaku.

*(26* ) Sarkin Zazzau Aminu ya nada dansa *Garba* Madakin Zazzau bayan rasuwan Madaki shehu.Sai dai Madaki Garba bai jimaba yace ga garinku.

*(27* ) Sarkin Zazzau Shehu Idris Ya nada dansa *Aliyu* Madakin Zazzau.Amma kaman dai Madaki Garba shima bai jimaba ya koma ga mahaliccinsa.

*(28)* Sarkin Zazzau Shehu Ya kuma nada dansa *Kabiru* a matsayin Madakin Zazzau.Madaki Kabiru ya rasu shima bada Jimawa ba.

*(29)* Idan muka lura za muga cewa tun daga *1804* har zuwa *2020* kimanin shekaru *216* Sarki dayane kawai na mallawa ya taba nada dansa Sarautan Madakin Zazzau.

*(30)* Zamuga Sarakunan bare-bari guda *6* sunba yayansu Sarautan Madakin Zazzau.Sarakunan Katsinawa guda *3* sunba yayansu Madakin Zazzau.

*(31* ) Bare-bari sunyi Madakin Zazzau sau *11.* Mallawa sunyi sau *4* katsinawa ma sunyi sau *4*

Na gani ne a wani Shafi na kwafa na turo a nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here