YA SHAFE SHEKARA 15 YANA GYARAN HANYA

0

YA SHAFE SHEKARA 15 YANA GYARAN HANYA

Misbahu Batsari
@Jaridar Taskar Labarai

Wani mutum mai suna Malam Lawal Gazgayi, mazaunin kauyen Dan-Geza, wani kauye mai nisan kilomita 10 da ke Arewa maso Yammacin Batsari ta Jihar Katsina.

Malamin ya shafe tsawon shekara fiya da 15 yana aikin sharewa da gyara hanyar garinsu, wadda ta tashi daga Batsari zuwa Dan-Geza.

Da yake hanyar birji ce, duk karshen damina wato bayan daukewar ruwan sama, tana cunkushewa da yashi da ramuka, wanda ke haddasa hadurran ababen hawa, musammun babura sakamakon lalacewar hanyar. Dalili ke nan da ya sa wannan bawan Allah ya daukar wa kansa wannan aiki na share ta da yin ciko inda ruwa ya yi rami tun daukewar ruwa har farkon damina na tsawon shekaru ba tare da la’akari da me zai samu, ko me zai same shi ba.

Ya labarta mana cewa, ya sha haduwa da fataken daji. Wani lokaci ma sukan sa shinge kusa da shi, amma cikin ikon Allah, ba su taba yi masa ko da kallon banza ba.

Sannan da muka tambaye shi ko akwai wani da ke biyan sa? Sai ya ce, gaskiya shi babu mai ba shi komai, sai dai dai-daikun jama’a, wanda ya yi niyya yakan ba shi dan abin da bai taka kara ya karya ba.

Shi dai wannan bawan Allah yana nan yana aikin sa a kan hanyar garinsu kullum tun daga Lahadi har Alhamis, Juma’a da Asabar ne kadai ba ya fita wannan aiki da yake yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here