Ahmad Musa zai gina Makarantar Boko a mahaifarsa da ke Jos

0

Ahmad Musa zai gina Makarantar Boko a mahaifarsa da ke Jos

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Shahararren dan kwallon kafa Nigeriya kuma Kaftin na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Ahmed Musa ya bayyana aniyarsa ta gina makarantar boko a garin Jos, ta Jihar Filato.

Ahmed Musa ya ce zai gina makarantar ce a yankin Bukuru da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, wanda anan ne aka haife shi kuma ya taso anan, domin kyautatawa al’ummar yankin.

Shahararen dan kwallon kafar ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram, inda ya ce “Ba zan manta da unguwarmu ba da kuma gudunmawar da ya kamata na yi wa al’ummarta.

See also  AN KAMA MACIJIN DA YA CIJI MAHADI SHEHU

Don haka nake murnar sanar da fara aikin gina makaranta M&S a jihar Filato a karamar hukumar Jos ta kudu a garin Bukuru, domin ilimi mabudi ne inji shi”

Ahmad musa wanda dan asalin jihar Filato ne ya buga wa kungiyoyi kwallon kafa a duniya da dama kamar Leicester City ta kasar Ingila.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here