Jam’iyyu 12 ne za su fafata a Zaben Kananan Hukumomi na Kano

0

Jam’iyyu 12 ne za su fafata a Zaben Kananan Hukumomi na Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kimanin jam’iyyun siyasa goma sha biyu ne suka fitar da ‘yan takarar su, gabanin zaben kananan hukumomin jihar Kano da zai gudana gobe.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan, cikin wata tattaunawa da manema labarai a karshen makon nan.

Garba Ibrahim Sheka na cewa tuni hukumar ta kammala duk shirye-shiryen tunkarar zaben kananan hukumomi a cikin watan nan na Janairu.

Yana mai cewar zaben zai gudana a kananan hukumomi 44, hade dana Kansiloli a mazabu 484 na jihar Kano.

Farfesa Sheka ya kara da cewa hukumar ta zauna da shugabancin jam’iyyun siyasa da kuma masu ruwa da tsaki, don kammaluwar zaben cikin tsarikan da aka shirya tun da fari.

“Ya zuwa yanzu mun raba kayayyakin zabe izuwa ofisoshinmu dake kananan hukumomi, yayinda nan bada dadewa kuma zamu kai sauran muhimman kayayyakin.

“Haka zalika mun horas da turawan zabe da sauran jami’ai, don tabbatar da sun yi ayyukan su yadda ya kamata.

“Shi kuwa samun nasarar zabe kokarin dukkanin bangarori ne zai haifar da hakan. A saboda haka muke neman goyon bayan masu ruwa da tsaki don yin zabe lafiya. A cewar Farfesa Sheka.

Shugaban ya kuma ja hankalin dukkanin jam’iyyu da su basu hadin kai, kafin da kuma bayan zaben.

A cewar Garba Ibrahim Sheka sama da kungiyoyi da cibiyoyi masu idanu 200 suka nuna bukatar shigowa don sanya ido yayin gudanar da zaben.

Ya kara da cewa hukumar na yin aiki kafada-da-kafada da kungiyoyi masu zaman kansu don kula da yadda jami’an mu za su tafiyar da harkokin zabe a mazabu 484.

“Sai dai akwai bukatar kungiyoyin suyi ayyukan su ba tare da ketare iyaka ba, da kuma dokokin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gindaya, a cewar sa.

Shugaban hukumar zaben ta jihar Kano KANSIEC na cewa hukumar tayi hadin gwiwa da rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro, don tabbatar da an yi zabe cikin doka da oda a jihar ba ki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here