Kungiyar Waiwaye adon tafiya ta yi bikin cika shekaru 6 da kafuwa

0

Kungiyar Waiwaye adon tafiya ta yi bikin cika shekaru 6 da kafuwa

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

A ranar litinin da ta gabata Kungiyar raya aladu da habaka al’adun Hausa mai suna Waiwaye adon tafiya, ta yi bikin shekara 6 da kafuwa gidan Makama da ke kusa da gidan sarkin Kano, kungiyar da jigo a masanartar Kannywood kuma mai unguwar Mandawari Alh Ibrahim Mandawri ya ke jagoranta,

ya yi kira da a farka domin dabbaka al’adun Hausawa dama sana’oinsu tun kafin lokaci ya kure, ya yi wannan kiran ne daidai lokacin da ake gudanar da taron kungiyar Waiwaye Adon Tafiya, wacce aka kafa ta don raya harshe da al’adun Hausa.
Ibrahim mandawari ya ce wannan kungiyar a cikin shekara shida samu Nasarori da dama cikinsu akwai shirya makaloli inda muke gayyato manyan Farfesoshi da Daktci na jami’o’in kasar nan, don haka kungiya ta kudiri aniyar maida wadannan makalu Littafi, ya kara da cewa kungiyar ta gabtar da makon Hausa a shekarar 2016, wanda shi ne na farko da wata kungiya ta aiwatar a wajen makaranta a Nigeriya, sannan kungiyar ta yi taron bajekolin Abincin gargajiya a gidan Makama a shekara 2019,

See also  AN GARKAME WASU MA'AURATA SABODA LAIFIN TILASTA 'YA'YANSU SU YI AZUMI.

Dr. Asiya Malam Nafiu Daga makarantar kwalejin Ilimi ta ta ray ya (FCE) ta gabatar da takarda mai Taken “ASAN MUTUN A KAN CINIKINSA” inda ta nuna muhimmancin sano’in Bahaushe da kuma kira ga hukumomi da a sanya hannu don ingantasu.

Haka kuma da yammacin ranar wannan kungiya ta shirya Gasar kacici-kacici akan Aladun Hausa, inda kungiyar Hausawan Afirka ta zo a mataki na farko sai Kungiyar zabi sonka ta zo a mataki na biyu, yayin da kungiyar Gizago ta zo a matsayi na uku.

Taron ya samu halartar manyan baki daban-daban ciki da wajan jihar kano, wadan da suka hadar: Alhaji Zakari Sadik Guda, wakilin kwamishina raya al’adu da yawon bude ido na jihar Kano, sai Dan Majen Kano kuma Hakimin Gwale Alhaji Yahya Inuwa Abbas, Farfesa Sai’idu Muhammad Gusau, Farfesa Yakubu Magaji Azare, Farfesa Aliyu Muazu Dr. Asiya Malam Nafi’u, Dr. Umma Aminu Inuwa da dai sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here