MAHADI SHEHU BAYA DA LAFIYA…..
Inji yan sanda
Muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Shahararren Dan kwarmaton nan, Alhaji mahadi shehu haifaffen katsina mazaunin Kaduna, baya da lafiya kamar yadda wata majiya a hukumar yan sanda ta kasa ta fada ma jaridun mu a jiya jumma a 15/1/2021.
Mahadi shehu ya kamata ya kai kansa hedkwatar yan sanda ta kasa a ranar litinin 11/1/2021.amma bai samu zuwa ba , kamar yadda aka tabbatar mana.
Majiyarmu dake ofishin hedkwatar yan sanda tace , mahadi shehu ya aiko lauyan sa da wasikar cewa ba zai samu damar zuwa ba saboda baya da lafiya.kuma yana kwance bisa shawarar likita da kuma amsar magani.
Majiyarmu tace yan sandan sun amshi wasikar kuma sun hada da takardun dake wajen su.sun rubuta rahoto sun tura ma babban sufeto janar na yan sanda na kasa don ya bada umurnin matakin da za a dauka gaba .
Yan sanda sunce wannan shine karo na biyu da ya ki zuwa wajensu.duk akan dalilai na rashin lafiya .sunce na farko ya aiko yace ya kamu da cutar covid 19 kuma ya kebe kansa da iyalanshi.
Sai kuma wannan karon da ya sake bada uzuri ta hanyar lauyan shi.
Majiyarmu ta yan sanda sun ce, sun fara gajiya da lamarin na binciken mahadi shehu don haka sun tsara yana zuwa su kai shi kotu a karkare maganar a can.
Zargin da yan sandan ke bincike , gwamnatin katsina ce ta kai korafin ga hukumar yan sanda ta kasa .akan mahadi shehu a bisa zargin kirkira takardun bogi,bata suna da tunzura jama a.akan haka hukumar yan sanda ke bincikensa.
Munyi kokarin jin ta bakin mahadi shehu ta wayoyinsa duk mun kasa samun sa don yi ma labarin adalci akan ikirarin yan sanda na baya da lafiya shi ya hana shi zuwa wajensu.
Mahadi shehu ya shafe watanni yana fallasa ga gwamnatin katsina a shafukan yanar gizo.yace kuma yana yi ne don a gyara
Hanyar da yake bi , hatta wasu malaman addinin musulunci sun soke ta. A katsina wasu na ganin shi gwarzo wasu kuma na kallonshi Dan kawo batanci.