YADDA MUTTAQA RABE YA TAIMAKI NAGOMA

0

YADDA MUTTAQA RABE YA TAIMAKI NAGOMA

@Jaridar Taskar Labarai

Shahararren Daraktan fina-finan Hausar nan, Ashiru Nagoma da ake yawo da hotonsa cewa ya samu rashin lafiya. An tabbatar mana cewa ya yi shekaru cikin wannan halin da yake ciki.

Daraktan, wanda ya yi tashe, kuma a lokacinsa, ba wani fim da ke iya ja da fim dinsa in har ya fitar. Yanzu yana cikin cikin muwuyacin hali.

Ashiru Nagoma ya yi sanadin tashe da daga wasu taurarin fim da yanzu suke tashe. Wasu kuma sun yi tashen har sun zama tarihi.

Jaridar nan ta yi magana da wasu masana a kan harka fina-finan Hausa da yadda labaransu ke tafiya, irin su mawallafin Kannywoodxclusive da wani tsohon Wakilin Mujallar fina-finai, duk sun tabbatar mana cewa, Nagoma ya yi shekaru yana fama da wannan matsalar.

Wani labarin da ba a fada shi ne, kokarin da Injiniya Muttaqa Rabe Darma ya yi na a yi masa magani ya samu lafiya.

See also  FG raises N742.56bn Sukuk fund for road projects

Muttaqa Rabe Darma Dan Katsina ne da ya yi suna wajen taimakon matasa masu hazaka, basira ko baiwa. Shi ne Shugaban dakin karatu da horo na PLEASANT LIBRARY da ke Katsina.

Muttaqa Rabe, ta hanyar wasu ‘yan fim ya rika sanya wa ana kai Ashiru Nagoma wajen masu magani, ko Allah ya sanya ya samu lafiya, amma abin ya ci tura.

Wadanda muka yi magana da su sun ce, Muttaqa Rabe ya dau lokaci yana wannan aikin alherin, daga baya ya hakura.

Wani darasi na rayuwa abin misali ga na baya shi ne, Ashiru Nagoma lokacin da yake tashen sa ya yi gadara, izgili, walakanci da nuna isa.

Wannan kuma wani darasi ne da ya kamata matasanmu su yi nazarin sa da daukar darasin da ke cikinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here