Mutum Miliyan 151 suke amfani da Internet a Nigeriya
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Hukumar kididdiga ta kasa MBS ta ce masu amfani da Internet a kasar nan sun karu da Miliyan 143 da dubu 63 zuwa miliyan 151 da dubu 51, a zango na biyu na shekarar da ta gabata,
Wanda hakan ke nuna cewa an samu karin kaso 4 da digo 59 na masu amfani da Internet a fadin Nigeriya,
Bisa kididdigar da aka fitar ya nuna cewa jihar Legas ta fi yawan masu aikewa da sakon murya ta kafar Internet a wannan tsukin da akai bita akansa, sauran kuma su ne jahohin Kano da Ogun.
Hukumar MBS ta tabbatar da cewa jihar Bayelsa da Ebonyi su ne suke matakin karshe na masu amfani da Internet a fadin Nigeriya.