MATA MARASA IMANI
mun Ciro daga shafin taskira H online
Jiya nakejin Labari a shirin Baba Suda na Dala FM cewa wata Uwar Gida ta kira Yarinyar da Mijinta zai Aura a waya cewa tanason suhadu zata bata Gudunmuwar Biki.
Ita Amaryar da ake shirin Aura batasan dawa take Magana ba, cikin Hilata dai Uwargida ta Hilaci Amaryar da Mijinta ke shirin Aura suka hadu a wani waje tasa Wuka tasoke ta a kirji da wuya a karshe rai yayi halinsa.
Shekaran jiya Hukumar Yan Sanda reshen Jihar Kano tabayyana wasu Kidnapers dasuka kama a unguwar Jaba, Mace ce ‘Yar Shekara 20-25 takama gidan haya suka tare aciki take yaudarar Samari tajasu takaisu Gidan arike su a nemi kudin Fansa.
Hoton Yarinyar nan dake kasa ance a Jihar Niger aka kamata da laifin Garkuwa da Mutane gatanan harda Bindiga aka kamata.
Wai ya akayi tausayi da Imani yafara kauracewa a zukatan Matan wannan Zamanin?
Kuma meyasa in an kama Mace da laifin Ta’addanci ko cin zarafin Miji ko kishiya bama ganin rubutun su Sayyada Rahma da sauran Mata masu ganin Maza suna zaluntar Mata?
Inama Matan Zamanin nan namu zasu koma kamar Matan damuka gada Zamanin Kaka da Kakanni?