Koyi Da Gwamna Masari Yasa Na Gina Hanyar Ruwa A cikin Unguwarmu

0

Koyi Da Gwamna Masari Yasa Na Gina Hanyar Ruwa A cikin Unguwarmu –Mai Turaka
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Mai taimakawa gwamna Masari akan wayar da kan jama’a akan abinda ya shafi gwamnatinsa Hon. Abdu;’aziz Mai Turaka ya mika hanyar ruwa (Kwata) da ya ginawa al’ummar daki tara ga dattawan unguwan domin cigaba da kula da ita don a samu bukatar da ake nema.
Da yake jawabin a wajan bikin mika wannan baban aikin Hon. Mai turaka ya bayyana cewa wannan aiki ya yi shi ne sakamakon maganar da mahaifiyarsa ta yi masa saboda rokon da mutanen unguwa suka yi mata na a taimaka a yi wannan aiki.
“Babu shakka wannan aiki na yi shi da niyar Allah ya kai ladan zuwa ga mahaifiyata, ke nan ya zama sadakatu jariya, duk da cewa tana nan da ranta, amma inason Allah ya kai ladan wannan aiki gareka” inji
Dangane da batun cewa gwamnati ce ta yi wannan aikin hanyar ruwa kuwa, Abdul’aziz ya ce babu wata gwamnati ko wani mutun a cikin wannan aiki, shi ne da kansa ya yi ba tare da neman gudunwa kowa ba kuma bau wanda ya bada wata gudjnmawa domin yin wannan aiki.
Mai Turaka ya yi bayanin cewa wannan abun da aka ga ya yi to koyi ne bisa koyi da yake daga mai girman gwamnan Katsina Aminu Bello Masari saboda a cewarsa Masari yana amfani da kudin aljihunsa wajan yin abinda zai taimakawa al’umma.
“Muna gani gwamna Masari yana gina Masallatai da Islamiyoyi da kuma aikin hanyar ruwa irin wannan da kudin aljihunsa ba sai ya yi amfani da kudin gwamnati ba, saboda haka wannan abun da muke yi koyi da shi” inji Mai Turaka.
Haka kuma ya yi addu’ar Allah ya kara zaunar da unguwar Daki tara lafiya, sannan ya yi kira ga dattawan da ya hannata wannan aikin gare su da su tabbatar da tsaftar wannan hanyar ruwa domin amfanin kansu da kansu.
Daga karshe ya yi alkawarin sanya fiyib din ruwa da zai ratsa wannan unguwa domin amfanin mutane sannan ya kara da cewa zai sa a gina rijiyar burtsatse da zata taimaka idan ba a mai dao ruwa a cikin unguwar.
Shima da yake nasa jawabin a madadin mutanen unguwar daki tara, Alhaji Hussain Batsari ya yaba da wannan korari na S.A Mai Turaka wanda ya samar da wannan hanyar ruwa da ta yi shekara da shekaru ana neman wanda zai yi ta, sai yanzu.
Ya kuma bada tabbacin cewa a madadin mutanen unguwa za su kula da tsaftar wannan unguwa ta hanyar kwashe duk wata leda ko kazanta da zata toshe hanyar ruwa a cikin wannan kwata.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya kai ladar wannan aiki ga Hajiya Mahaifiyar Mai Turaka sannan ya roki Allah yasa Mai Turaka ya gama da Hajiya lafiya, ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su yi koyi da shi wajan samar da ire-iren wadannan ayyuka na alheri a cikin al’umma

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here