AN KAMMALA FIM AKAN YAN FASHIN DAJI

0

AN KAMMALA FIM AKAN YAN FASHIN DAJI
…..Wanda gwamnatin katsina ta dau nauyi
…..komai fim din ya kumsa?
Daga zaharadden Abubakar
Wani Kamfanin shirya fina finan hausa dake Kano mallakar wani Dan asalin katsina mai suna sani sani sule katsina, ya kammala tsaf da daukar wani fin akan barayin daji , Wanda aka Sanya ma fim din suna Makahon daji.
Gwamnatin katsina ce ta dau nauyin fim din kaco kam .kamar yadda takardun bukatar kamfanin na tayi fim din ga gwamnatin katsina, Wanda jaridar katsina city news ta samu suka tabbatar.
Kamfanin ya rubuta ma gwamnatin katsina ,ita kuma ta amince da sakin kudi don aikin.
Katsina city news sun ga hatta takardun bada umurnin a biya kamfanin kudin da a shirya fim din. Da kuma yadda aka biya kudin .
An biya kamfanin kudin sa baki daya cas, sannan ya fara daukar fim din a wasu bangaren jihohin Kano, katsina da jigawa.
Wadanda suka San yadda aka dauki fim din sunce an kammala daukar fim yanzu ana tace shi ne.kafin a sake shi ga al umma su gani.
A labarin da aka baiwa gwamnatin katsina za a yi fim din dashi.wanda jaridar katsina city news suka gani, in ba a gyara shi ba akwai inda keda matsala. Wanda bai dace ya fito a fim din ba.
Komai fim din ya kumsa? Ance an chanza labarin na asali,sai ya fito aga inda ya dosa.
Katsina city news sun tuntubi Wanda ke Pshirya fim din, Alhaji sani sule katsina ya tabbatar mana da kammala fim yanzu ana tacewa.
Yace za a fara fitar da tsakure na fim din a yada shi kafin a saki cikakken sa.fim din ya tara fitattun yan wasa da kuma sabbin idanu. Ya kuma samu hadin kan jami an tsaro Wanda suka bada kayan aikin da aka shirya fim din .
Hade da labarin nan akwai hotunan sashen daukar fim kamar yadda muka samo su daga wajen mawallafin kannywood xclusive isah bawa doro..

See also  Iyalin Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Shehu Kangiwa sun saida tsagin gidansa saboda talauci


________________________________________________
Katsina city news na a bisa yanar gizo www.katsinacitynews.com tana da yan uwa jaridar taskar labarai www.taskarlabarai.com da kuma the links news @ www.thelinksnews.com duk karkashin matasa media links nig Ltd duk sako a aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here