BA WANDA YA FI KARFIN JAM IYYA A APC

0

BA WANDA YA FI KARFIN JAM IYYA A APC
….Tsarin mulkin jam iyya zai aiki akan kowa
___________________________inji gwamnan katsina
@ katsina city news
Gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari yace jam iyyar APC da kundin tsarin mulkin ta na gaba da kowa In dai shi halastaccen dan APC ne.
Alhaji Aminu Bello masari yana magana ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam iyyar na duk fadin jahar a dakin taron masaukin shugaban kasa dake gidan gwamnatin katsina.
Yace kwanan nan ina nazarin kundin tsarin mulkin jam iyya inda na ga muna sakaki da bin shi don haka yanzu dole a dauko shi yayi aiki akan kowa.har da ni Aminu bello masari.
Gwamnan ya jaddada cewa Sam ba zamu amince da kafa wata kungiya a cikin APC ba.in kana ciki baka fahimci wani abu ba,kayi tambaya a yi maka bayani.amma kafa kungiya kaza da kaza ba zamu amince da wannan ba.
Akan rijista yan jam iyya gwamnan yayi rokon da ayi adalci yace ba wani Dan jam iyya dake neman rijista da za a kyale.
Gwamnan yayi addu ar Allah ya kawo wani gwamna a cikin a APC a katsina Wanda zai yi aiki fiye dashi.wanda za a rika tuna shi da kuma jam iyyar ta APC.
Gwamnan yace a siyasa tun 1992 Muke a ciki babu abin da bamu gani ba ba kuma darasin da bamu samu ba.don ina Baku shawarar ku tsaya inda kuke ku gyara jam iyyar ku.
Yaja hankalin manyan yan siyasa, su bar daukar jita jita daga yaransu, su kuma bar dogara da duk abin da suka gani a social media. Yace abin da Allah ya tsara ba Wanda ya isa ya chanza shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here