JAM’IYYAR APC TA KACAME A KATSINA

0

JAM’IYYAR APC TA KACAME A KATSINA

…An kafa sabuwar APC cikin APC

Mu’azu Hassan
@ katsina city news

Yanzu haka jam’iyyar APC na neman darewa gida biyu a Jihar Katsina, inda wasu jiga-jigai a cikinta suka yi nisa wajen kafa wata APC a cikin jam’iyyar ta APC, wadda har yanzu ba su bai wa tafiyar tasu suna ba, amma wasu na kiranta da APC A Sake Lale.

Wasu takardun da Editan jaridun Katsina City News ya gani, ya ga jadawalin sunayen membobin wannan kungiyar mai son kawo gyara a cikin jam’iyyar ta APC.

Takardun sun kunshi shugabannin wannan kungiyar na riko, wanda suka kama daga Shugaba na Jiha, zuwa masu taimaka masa su tara.

Wasu takardun suna kunshe da sunayen Wakilan shugabannin mutane uku-uku daga kowace Karamar Hukuma a cikin Kananan Hukumomi 24 na Jihar Katsina. Akwai sunan kowa da lambar wayarsa.

Wata takardar kuma ta kawo sunayen ‘yan kwamitin amintattu wannan tafiya da muka kira da sunan CHANJI A CIKIN APC.

Sunayen sun hada da jiga-jigai a cikin jam’iyyar, wadanda suka yi mata aiki, suka sadaukar, kuma yanzu suke ganin jam’iyyar na tafiya ba daidai ba.

Sun sha alwashin ba su zuwa ko’ina, suna nan a cikin jam’iyyar sai an gyara ta.

A cikin sunayen akwai hamshakan Attajirai da wani Janar na soja mai ritaya da wasu tsaffin Sanatoci da wani tsohon babban jami’in ‘yan sanda da wasu tsaffin ‘yan takara daga Gwamna, zuwa wasu mukaman da sauransu.

Mun tuntubi wasu da muka ga sunayensu a cikin jadawalin, sun tabbatar wa da jaridar nan cewa, suna cikin tafiyar ne don neman kawo adalci da dimorakadiyya a cikin jam’iyyar.

Sun ce jam’iyyar APC ta kauce daga bisa tubar da aka gina ta, don haka suka fara motsi tun yanzu.

Suka kara da cewa, wasu shugabannin jam’iyyar sun zama masu son kansu da kansu da azurta kansu, tare da watsi sauran wadanda suka sadaukar da lokaci da dukiyarsu, aka yi wahala da su wajen kafuwar ta.

Bincikenmu ya tabbatar da cewa, membobin wannan kungiyar suna ta tattaunawa da nufin daukar matsaya da matakan da za su dauka nan gaba.

Akwai yiwuwar nan gaba kadan su yi taron manema labarai don bayyanar da kansu da manufofinsu da jadawalin matakan da za su dauka daki-daki kuma filla-filla.

Mun yi kokarin jin ta bakin shugabannin APC na Jiha a kan wannan sabon motsi, amma babu wanda ya dauki wayarmu, ko ya ba da amsa ga sakon da muka aika masa ta waya.

Mun aika wa Shugaban jam’iyya na Jihar Katsina, Malam Shitu S. Shitu sakon waya, amma babu amsa.

Mun aika sakon ga Kakakin jam’iyya, Alhaji Abu Gambo Dan Musa, shi ma babu amsa.
________________________________________________
Kamfanin matasa media links ya mallaki jaridun taskar labarai dake www.taskarlabarai.com. da katsina city news dake a www.katsinacitynews.com da kuma the links news @ www.thelinksnews.com duk sako a aiko ga 07043777779.email.katsinaoffice@ Yahoo.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here