Masharurin Marubuci kuma Danjarida ya kwanda Dama
Daga Ibrahim Hamisu
Larry King, mashahurin marubuci ne, mai gabatar da shirye-shirye a gidajen talabijin da radio a Amurka.
Mai shekara 87, King ya kwashe tsawon shekaru 60 yana tsakanin rubutu da gabatar da shirye-shirye a talabijin.
Shekara 25 ya kwashe yana gabatar da wani shirin tattaunawa da ‘yan siyasa, masu wasanni da fitattu a fanno daban-daban a gidan talabijin din CNN.
Shirye-shiryensa na Larry King Show da Larry King Now, sun yi sharafi a shekarun sabi’inino a gidaje rediyo da talabijin na kasashen duniya daban-daban. Miliyoyin jama’a ke kallo da sauraro.
Tun daga shekarar 1985-2010, Larry King ya rika gabatar da wani shirin hira da baki a CNN, Miliyoyin jama’a ke kallon shirin a akwatunan talabijin dinsu.
Ya kwashe tsawon shekara 20 yana rubutu a mashahuriyar jaridar nan da ake kira USA Today. Babban bango ga marubuta a duniya.
Ya rasu yau Asabar a wani asibiti da ake kira Cedars-Sinai Medical Center da ke Los Angeles sakamakon kamuwa da cutar Korona, kamar yadda kafar Ora Media ta sanar.