Miliyan 25 ne kudin Fansan ‘Yan Kasuwar kantin Kwari

0

Miliyan 25 ne kudin Fansan ‘Yan Kasuwar kantin Kwari

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Yan kasuwar Kantin Gwarin nan su 18 da aka yi Garkuwa da su akan hanyarsu ta zuwa Aba sun Shaki iskar yanci bayan an biya kudin fansa Naira Miliyan 25,

Mutane biyu ne dai suka jagoranci karbo wadannan mutanen Abba Hamza Ayagi da Mukhtar Sani Dala su ne sukai ta Dawainiyar harhada kudaden, bayan hada kudin kuma suka tafi kafa da kafa har wancan dajin na jihar Edo suka mikawa masu garkuwa da mutane kudin, sannan aka sallamo su,

Da aka tambayi Hamza Dala ko gwamnati ce ta sa aka sako su? sai ya ce ” ta bangaren Gwamnatin Kano duk wanda ya ce an bada wani abu na taimako to ya tuntubi wanda ya bawa a kawo mana don mu baa ba mu komai ba daga Gwamnati, ni da mukhtar Sani rak ne muka karbosu a lokacin da ake hada kudin duk guduwa akai aka barmu haka muka tafi cikin kungurmin da ji muka kai kudin a cikin buhu”

See also  Tarihin Rayuwar Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano

A gefe guda kuma, shugaban yan kasuwar Kantin Kwari Mal. Muhammadu Bello na cewa Gwamnatin Kano da hukumar kasuwa ne suka shiga suka fita wajen ganin an ceto yan Kasuwar,

Yanzu haka dai wadannan yan kasuwa na kantin Kwari na wajen likitoci na duba su.

Masana tattalin arziki anan Kano dai na nuna dauwarsu akan yadda har ya zuwa yanzu wadannan yan kasuwa suka kasa samun tallafin da ya kamata daga hukumomin jiha da na tarayya.

Akwai bukatar kungiyyin fulani su hada hannu da kungiyoyin tsaro a Nigeriya, domin dakile yadda wasu daga cikin Fulani ke rungumar sana’ar garkuwa mutane a matsayin sana’a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here