Tsohon kwamishinan Ilimi na jihar Kano ya Rasu
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Allah yayiwa tsohon Kwamishinan ilmi na tsohuwar jihar Kano da Jigawa rasuwa, Alhaji Abdulhamid Hassan.
Anyi jana’izar yau Talata, da misalin karfe 4 na yamma a gidansa dake Unguwar NNDC.
Daga cikin ‘ya’yan da ya bari akwai Alhaji Hassan Abdulhamid Hassan, shugaban hukumar kare hakkin mai saye ta kasa ofishinta dake nan Kano.
muna Addu’ar Allah yayi masa rahma yasa aljanna makoma!