DAKATAR DA SABO MUSA HASSAN TSAKANIN JAM IYYAR PDP DA APC A KATSINA

0

DAKATAR DA SABO MUSA HASSAN
TSAKANIN JAM IYYAR PDP DA APC A KATSINA
Sharhin taskar labarai.
muazu hassan
@ jaridar taskar labarai
Daya daga cikin manufofin da aka kafa jaridun taskar labarai shine, tabbatar da yin dimorakadiyya da adalci a cikin jam iyyu. Karfafa su da kuma Sanya masu ido.Saboda sune tsani na kama mulki.sune zuciya a siyasa.in ta baci duk gangar jiki ya baci.
Mafi yawan matsalolin da gwamnatoci kan samu na farawa ne daga rashin adalci daga jam iyya ya kai har ga kafa gwamnati.
Kwanan nan manyan jam iyyun katsina, sun fuskanci matsaloli masu kama da iri daya. A PDP wasu sukayi taro suka yi Kira da jam iyyarsu ta gyara wasu matsalolin dake fuskantarta.
Taron ya samu yaya tawa a kafofin watsa labarai na ciki da wajen kasar nan.
Jam iyyar ta dau mataki akan duk wadanda ake gani sune shugabannin taron.misali a katsina. Dutsinma , kurfi , kankia da safana. Daga baya jam iyyar ta koma tattaunawa da ya yanta don gano bakin zaren.
A jam iyyar APC satin da ya gabata wasu yan jam iyyar APC suka gudanar da taro a Kano.a taron suka yi koke akan wasu matsalolin da suke son a gyara cikin jam iyyar.
Sun shelanta cewa.gyara suke Kira ba ayi fada ba.suka yi jinjina da yabo ga gwamnatin APC.suka ce a cikin jam iyya suke son ayi gyara.
A taron ga bidiyo ga hotunan masu taron ga abin da suka ce.
Jam iyya bata ji dadi ba.mutum daya shine sabo Musa aka aika ma takardar gayyata shi daya aka dakatar.
A karamar hukumar katsina, bashi kadai yaje ba, bashi kadai ne jami in gwamnatin jaha da ya halarta ba.an zo daga kananan hukumomin 34.
Shugabannin riko na tafiyar sun fito daga kananan hukumomi 11.
Me ya Sanya sabo Musa kadai aka dakatar? Sashen tsarin mulkin jamiyya da aka ce, sabo Musa ya Saba, ya shafi duk wadanda sukaje wannan taron.
Ya kamata jam iyyar tayi adalcin daukar mataki akan duk Wanda yaje taron nan.ko tayi gaggawan janye dakatarwar sabo Musa. Wannan shine adalci.
________________________________________________
Taskar labarai na a bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779 Kira 081377777245 email katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here