Gwamnatin Kano ta dakatar da sheikh Abduljabbar daga yin Wa’azi

0

Yanzu-Yanzu : Gwamnatin Kano ta dakatar da sheikh Abduljabbar daga yin Wa’azi

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da Sheikh Abduljabbar sheikh Nasiru Kabara daga yin wa’azi, tare da bada umarnin rufe masallacinsa da ke filin mushe a karamar hukumar Gwale,

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a daren Laraba.

Kwamishinan ya ce an dauki matakin kulle masallacin ne saboda dalilan tsaro.

Sannan gwamnati ta umarci kwamishinan yan sanda na jiha tare da jamian tsaro da su tsaya suka an aiwatar da wannan umarnin na gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here