Garuruwa kusan 50 sun tashi a Faskari

0

TSUGUNNE BATA ƘARE BA

Garuruwa kusan 50 sun tashi a Faskari

Daga Auwal Jibril ‘Yankara

@Taskar labarai; www.taskarlabarai.com

Har yanzu tsugunne bata ƙare ba a kan lamarin tsaro a jihar katsina, musamman a ƙananan Hukumomin Faskari, Sabuwa, da Ɗandume.

Kusan kullum sai ansamu labarin garuruwan da ‘yan bindiga suka shiga suka kashe mutane, ko suka kwashe su domin neman kudin fansa, ko su kore dabbobin da suka mallaka.

Garuruwa na baya-bayan nan da ‘yan bindigar suka je sun haɗa ƙauyen ‘yar Daura dake kusa da garin ‘yan kara inda sukayi gaba da mutum 11 duka mata Daga bisani sun nemi abasu Naira miliyan 10. Bayan ancimma yarjejeniya, an biya su, kana suka sako su.

Ƴan bindigar sunje wasu garuruwa da suka hada da Unguwar Gizo, Unguwar Biri, Fankama, ‘Yar Itace, Tsuru, Mangwarori da sauran su, inda suka kore ma su ɗaruruwan Shanu da tumakai a wani garin ma harda kaji.

Ƴan bindiga sun kashe mutane 10 a Unguwar Sarki, biyar a Gidan Sarkin Makafi uku a Ɗankaya da wasu biyu a Jarkuka Mutum duk a Ƙaramar Hukumar Faskari.

Haka al’amarin yake a Ƙaramar Hukumar Sabuwa da Ɗandume, inda ya zuwa yanzu kuma kusan duk wani ƙauye dake cikin lungu sun fashe sun dawo garuruwan da ke bakin hanya don tsira da rayuwarsu.

A kwanaki biyu a jere ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyukan ‘Yar tasha da Kwana duƙe da kuma mazaɓar Tumburka a Ƙaramar Hukumar Ɗandume da kuma Doka da Garawa a Ƙaramar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, inda suka tafi da mutane da dabbobi.

Haka nan sunje ƙauyukan Ɗanƙaya inda suka kashe mutum 3 ciki harda Jariri du a Unguwar Hayaƙi a mazaɓar Sheme a Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Wannan na faruwa ne duk da ɗimbin jami’an tsaron da aka jibge a sansanin soja na Faskari da ‘yan sandan kwantar da tarzoma da rundunar zaman lafiya dole ta Ɗan Zaki yaran marigayi Ali Ƙwara.

Duk da ɗimbin ‘yan gudun hijirar da kusan kullum suke kwararowa garuruwan dake bakin hanya, irin Faskari, ‘Yankara, Sheme, da Mairuwa, amma ba wani tanadi da akayi don akula da rayuwarsu da ta iyalansu, sai dai mutum ya tafi inda danginsa suke ko ya kama hayar wurin zama shida iyalan sa.

A ƙasa ga jerin garuruwa 28 da suka fashe babu kowa cikinsu.

1.Unguwar Biri, 2.Unguwar Yaro, 3. Unguwar Ɗan Tasa, 4. Unguwar Ɗanboka, 5. Unguwar Sarki, 6. Unguwar Sarkin makafi, 7. Kafi Dogon Gida, 8. Ƙurmin, 9. Jarkuka, 10. Kamfanin Mai lafiya, 11. Tsuru, 12. Kwantai, 13. Kuka Shida, 14. Kadisku, 15. Fankama, 16. Zagami, 17. Kurmin Doka, 18. Unguwar Malam, 19. Unguwar Mai dawa, 20. ‘Yantuwaru, 21. Ɗan Aji, 22. Mai Sabo, 23. Bargaja, 24. Matseri, 25. Unguwar Gizo, 26. Unguwar Maigiya, 27. Gidan Alhaji Ado, 28. Matseri, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here