SHARRI DA KAGE AKA YI MANI In ji Sameer Isma’il

0

SHARRI DA KAGE AKA YI MANI

In ji Sameer Isma’il

@Katsina City News

Alhaji Sameer Isma’il Yarima Musawa, kuma Sanyinnan Katsina, ya karyata wata murya da ke yawo, wadda aka ce daga wajensa ne da sunan murya ce ta karya da kage da nufin batawa da ci masa fuska.

Yarima, wanda ke bayyana haka a ganawar da ya yi da manema labarai a ofis dinsa da yammacin yau Lahadi 7/2/2021 a Katsina, ya tabbatar da cewa wannan murya kage ce da sharri.

Ya ce wadanda suka tsara makidar, sun yi ne da nufin cimma manufar bata suna da haddasa husuma da kuma bata shugabanni, kuma iyayenmu a Jiha, Kasar da ma Duniya baki daya.

Sanyinnan Katsina ya kara da cewa, sam ba tarbiyyarsa bace, kuma ba halinsa ba ne, bata shugabanni, ko cin fuskarsu.

See also  Kwamishinan Ilimi ya sauke kungiyar shugabannin makarantu sakandare a zamfara

Sanyinnan na Katsina, ya saki wani bidiyo wanda a cikinsa yake kara baranta kansa da wannan muryar da ke yawo.

A jiya ne wata murya ta rika yawo, wanda a ciki aka ji ana fadin wasu maganganu marasa dadi da ba da misali maras kyau ga wasu manyan da ke a cikin Jahar Katsina.

Wasu da ake zargin ‘yan adawar Yarima ne, sun dandaganta shi da muryar, yayin da shi kuma ya nisanta kansa da ita.

Sanyinnan na Katsina, ya roki duk masoyansu su kwantar da hankalinsu. Ya jaddada cewa makiya ba za su taba yin nasara ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here