AN CIRE MA SAMIR SARAUTAR MUSAWA

0

AN CIRE MA SAMIR SARAUTAR MUSAWA
@ Katsina city news

Sarkin musawan katsina Alhaji sagir Abdullahi inde ya janye sarautar yariman musawa wadda Samir isma il ke rike da ita.
Sarkin ya shelanta sanarwar ne a wata takarda da ya fitar a yau Talata mai kwanan wata 8/2/2021da taken takardar janye Sarautar yariman musawa.kuma sarkin musawa da kansa ya Sanya mata hannu.
A takardar ance yanzu Samir baya da wata alaka da gidan sarautar ta musawa.
Samir dai ya shiga matsala ne bayan wata murya ta fito yana wasu maganganu marasa dadi akan sarkin katsina da gwamnan katsina da Dahiru mangal.
Muryar da samer yace kazafi ake masa a wani taron manema labarai da yayi a karshen satin da ya wuce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here